Bangaren siyasa da zamantakewa; wakilin majalisar koli ta musulmi a kasar Etiophiya ya bayyana cewa: Imam Huseini (AS) ya sadaukar da raid a rayuwarsa domin tabbatar da adalci kuma ta wannan hanya ce ya yada addini na gaskiya da ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da ayalan gidansa ya zo da shi ga musulmin duniya.
Kamfanin dillancin labarai na ikana da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: wakilin majalisar koli ta musulmi a kasar Etiophiya ya bayyana cewa: Imam Huseini (AS) ya sadaukar da raid a rayuwarsa domin tabbatar da adalci kuma ta wannan hanya ce ya yada addini na gaskiya da ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da ayalan gidansa ya zo da shi ga musulmin duniya.A lokacin wani taron Ashura da farkawar musulmi da ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci tai ran a birnin Adis Abeba fadar mulkin kasar Etiophiya inda aka samu halartar malamai da matasa masoya ahlul Baiti (AS) da iraniyawa mazauna wannan kasa da kuma yan shi'a yan kasar ta Etiophiya Indiyawa da yan Pakistan haji Kamil Sharif ya bayyana haka da kara cewa: Imam Huseini (AS) ya koyar da bani Adam muhimmacin sadaukar da kai da kuma zama abin koyi ga duk wani dan gwagwarmaya kan kawar da zalunci da danniya musamman mashahuriyar maganarsa ni na fit one domin kawo gyara a cikin al'ummar kakana don kawar da fasadi da zalunci.
914522