IQNA

An Yawaita Taruka Kan yadda Karbar Binin Najaf Matsayin Fadar Al'adu

Bangaren kasa da kasa: ofishin hulda da jama'a a ma'aikatar al'adu a Iraki ya yawaita gudanar da taruka da zama na musamman kan yadda za a karbi bakunci da shirye-shiryen karbar matsayin da aka bawa birnin Najaf matsayin fadar al'adu ta kasashen duniya na musulmi a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu miladiya .



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: ofishin hulda da jama'a a ma'aikatar al'adu a Iraki ya yawaita gudanar da taruka da zama na musamman kan yadda za a karbi bakunci da shirye-shiryen karbar matsayin da aka bawa birnin Najaf matsayin fadar al'adu ta kasashen duniya na musulmi a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu miladiya . A kowace shekara ana zabar wani birni daga cikin manyan biranai na kasashen musulmi musamman ma biranai da suka yi suna ta fuskara tarihi da al'adu da zama babban birni na al'adu na kasashen musulmi da musulmin da kuma wannan karo aka zabi birnin Najaf na kasar Iraki domin ba shi wannan matsayi.

915469