IQNA

Taro Mai Taken Musulunci Da Matasa A Yau A Nigeria

Bangaren tunani da ilimi: ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci a tarrayyar Nigeriya tare da hadin guiwar bangaren yada addini na kasa da kasa sun shirya wani taro mai taken musulunci da Matasa a yau a Nigeria kuma a yau alhamis ashirin da hudu ga watan azar na shekara ta dubu daya dadri uku da tis'in hijira shamsiya za a fara gudanar da wannan taro.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa:

ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci a tarrayyar Nigeriya tare da hadin guiwar bangaren yada addini na kasa da kasa sun shirya wani taro mai taken musulunci da Matasa a yau a Nigeria kuma a yau alhamis ashirin da hudu ga watan azar na shekara ta dubu daya dadri uku da tis'in hijira shamsiya za a fara gudanar da wannan taro.Wadanda za su gabatar da jawabi a gurin wannan taron za su yi bayani kan kan dalilin day a sa ba a samin tarbiya daidai da koyarwa addini ga yayanmu a kasashen musulmi da kuma hanyoyin bi na ganin an inganta tarbiya ga yayan musulmi a tsakanin kasashen musulmi da kuma a dabra da haka dubi kan makircin da makiyan musulunci ke kullawa musulmi da kokaran canja akalar tarbiyar yaya da matasan musulmi .

915902