Bangaren kasa da kasa, da jijjifin safiyar yau ne wasu yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra’ayi suka kai hari kan wani masallaci a birnin Qods mai alfarma inda suka kone masallacin domin muzgunawa mabiya addinin musulunci.
Kamfanin dilalncin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CPI cewa, a safiyar yau ne wasu yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra’ayi suka kai hari kan wani masallaci a birnin Qods mai alfarma inda suka kone masallacin domin muzgunawa mabiya addinin musulunci da sauran palastinawa mazauna yankin.
Tun a cikin makon da ya gabata ne yahudawan sahyuniya suka rufe wata hanya da musulmi suke bi domin isa masallacin Qods, kuma sun dauki wannan mataki ne da sunan cewa yana daga cikin irin matakan tsaro da suke dauka a birnin Qods, amma kuma wadanda suka kai harin dukkaninsu yahudawa ‘yan kaka gida da suke zaune acikin yankunan palastinawa.
A safiyar yau ne wasu yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra’ayi suka kai hari kan wani masallaci a birnin Qods mai alfarma inda suka kone masallacin domin muzgunawa mabiya addinin musulunci da sauran palastinawa mazauna birnin Qods mai alfarma.
915807