IQNA

Hukumar Tuntubar Juna Ta Musulmi Ta Yi Allah Wadai da Bude mashigar Sha'afat A Kudus

Bangaren kasa da kasa;Ikmalul Dine Ihsan Uglo babban sakataren Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya yi Allah wadai da babbar murtya kan matakin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta dauka na bude mashigar Shaafat a arewacin kudus da suka mamaye.





Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Ikmalul Dine Ihsan Uglo babban sakataren Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya yi Allah wadai da babbar murtya kan matakin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta dauka na bude mashigar Shaafat a arewacin kudus da suka mamaye.A cikin wata sanarwa da kungiyar hadin kan musulmi ta fitar dangane da wannan labarin na bude mashigar da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi,babban sakataren kungiyar ya cewa: sake bude wannan mashigar mani makirci ne na gwamnatin harammatcciyar kasar Isra'ila na canja fuskar birnin Kudus da kuma raba Palasdinawa dubu sattin da biyar da yankin gabacin wannan birni mai muhimmanci da tarihi.

916540