Bangaren kasa da kasa: a lokacin da rana ta fito da haskaka na bayyanar Imam Khomeini ® da yadda ya tunkari ma'abuta girman kai da danniya da kuma jaruntakar da ya nuna na tunkrar yan mulkin mallaka da bukatar karewa sauran al'ummomin hakkokinsu da ake dannewa to a yau hasken wannan jan aiki mai muhimmanci nasa ya haskaka al'ummomin musulmi kamar Iraki .
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a lokacin da rana ta fito da haskaka na bayyanar Imam Khomeini ® da yadda ya tunkari ma'abuta girman kai da danniya da kuma jaruntakar da ya nuna na tunkrar yan mulkin mallaka da bukatar karewa sauran al'ummomin hakkokinsu da ake dannewa to a yau hasken wannan jan aiki mai muhimmanci nasa ya haskaka al'ummomin musulmi kamar Iraki .Wannan ya yi daidai da aya ta sha bakwai ta suratul nBakara . A yau malamai da sauran masana da marubuta da malaman tarihi da ke bin diddigin abubuwan da suka faru a baya sun yi ammana da cewa abin da imam Khomeini ® ya yin e ake ganin nasara da sakamakonsa a yau a kasashe da daman a musulmi na juyin juya hali da neman kawo sauyi da bujirewa gwamnatoci da shugabanni da ke tafiyar mulkin kasashensu karkashin karbar umarni daga kasashen yan mulkin malllaka da bin manufofinsu ido rufe kai da fata.Kuma duk da kokarin da wasu ke yi dare da rana na ganin sun kullawa musulmi makirci dad a canja akalar wannan gwagwarmaya da farkawa daga barci da musulmi suka yi ba za su cimma nasara ba sai ma abin day a cig a ko shakka babu.
915815