IQNA

Taro Kan Addini Domin Tabbatar Da Sulhu A Kore Ta Kudu

Bangaren nazari da ilimi: a karon farko za a gudanar da taron addini domin tabbatar da sulhu a Koreya ta Kudu tare da hadin guiwar cibiyar tattauanwa da fahimtar juna ta fatar baki ta addinai da kuma kungiyar hadin kan kasashen musulmi aka shirya wannan taron.




Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a karon farko za a gudanar da taron addini domin tabbatar da sulhu a Koreya ta Kudu tare da hadin guiwar cibiyar tattauanwa da fahimtar juna ta fatar baki ta addinai da kuma kungiyar hadin kan kasashen musulmi aka shirya wannan taron.A yau ashirin da bakwai ga watan azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya da misalign karfe uku na ranar yau agogon kasar ta Koreya ta kudu a dakin taro na Hauza za a fara gudanar da wannan taron da malamai dam asana da marubutta da malaman jami'o'I da cibiyoyin ilimi za su halarta domin bayar da bahasi da jawabai kan hanyoyin samara da sulhu mai daurewa a tsakanin kasashe da addinai daban daban na duniya.


916855