Bangaren siyasa da zamantakewa: a ranar ashirin da hudu ga watan Dai mai kamawa na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya daya yi daidai da cika kwanaki arba'in da zagayowar ranar da imam Huseini (AS) ya yi shahada tare da iyalan gidansa da sahabbansa a yankin karbala za a gudanar da taron tunawa da kwanaki arba'in na shahadar Imam Huseini (AS) a jamhuriyar Congo.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a ranar ashirin da hudu ga watan Dai mai kamawa na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya daya yi daidai da cika kwanaki arba'in da zagayowar ranar da imam Huseini (AS) ya yi shahada tare da iyalan gidansa da sahabbansa a yankin karbala za a gudanar da taron tunawa da kwanaki arba'in na shahadar Imam Huseini (AS) a jamhuriyar Congo.Sheikhu Isa Embaki daya daga cikin wadanda suka kammala karatunsu a Hauza kuma makaddashin cibiyar kula da al'adu a jam'ar Almustapha (SWA) al'alam reshenta da ke kasar ta Congo ya fitar da wannan bayani da a ciki yake cewa: yan shi'a a wannan kasar tuni suka yi nisa a shirye-shiryen gudanar da taron a wannan rana ta tunawa da cika kwanaki arba'in da irin wannan rana ta shahadar Imam Huseini (AS) da sahabbasa da iyalan gidansa.
916812