Bangaren kasa da kasa, a cikin wani rahoto da kungiyar kare hakkokin mata da kananan yara ta UNICEF ta fitar ta yi ishara da cewa haramtacciyar kasar Isra’ila tana cin zarafin kanan yara muslmi palastinawa da shekarunsu ba su wuce goma ba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadrawa na Palestine Info cewa, wani rahoto da kungiyar kare hakkokin mata da kananan yara ta UNICEF ta fitar ya yi ishara da cewa haramtacciyar kasar Isra’ila tana cin zarafin kanan yara muslmi palastinawa da shekarunsu ba su wuce goma ba zuwa sha wani abu ko kasa da goma.
A bangare guda kuma wani marubuci daga cikin haramtacciyar kasar Isra’ila mai suna Yusuf Shaddad ya bayyana cewa irin matakan da haramtacciyar kasar yahudawan take dauka na hana kiran salla a cikin yankunan palastinawa nau’i ne na wariya da ake nuna ma al’ummar palastinu a cikin yankunansu.
Yahudawan sahyuniya sun jima suna daukar matakai na takurawa kan palastinawa ba tare da wani ya isa ya ce musu uffan ba, domin kuwa duk abin da suke aikatawa suna samun kariya da goyon baya daga gwamnatocin Amurka da na kasashen yammacin turai.
918608