IQNA

Mai Tarjamar Kur’ani Kafin Sanin Yarukan Tarjama Dole Ya Zama Mai son Kur’ani

14:50 - December 21, 2011
Lambar Labari: 2242928
Bangaren kasa da kasa, mai tarjamar kur’ani mai tsarki kafin sanin yarukan da zai yi tarjama da su dole ne ya zama mai son kur’ani mai tsarki domin ta hakan zai iya yin aikinsa cikin nishadi da mayar da hankali ga abin da yake tarjamawa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, wata mai tarjamar kur’ani daga farisanci zuwa turanci Ma’suma Yazdan Panahi ta bayyana cewa, mai tarjamar kur’ani mai tsarki kafin sanin yarukan da zai yi tarjama da su dole ne ya zama mai son kur’ani mai tsarki domin ta hakan zai iya yin aikinsa cikin nishadi da mayar da hankali ga abin da yake tarjamawa musamman kur’ani mai tsarki da yake da usulubi na hikima da ta wuce ta dan adam.
Kamar yadda aka fada a cikin bayanin ayar da ta gabata, manzon Allah (SAW) ya umurci dukkanin musulmi da suka halarci yakin Uhud da su kara daura damara domin tunkarar rundunar mushrikai da suke nufin afkawa birnin madina, hakan ya sanya hatta wadanda suka ji raunuka ba a bar su a baya ba wajen aiwatar da wannan umurni na manzo.
Hakan ya jefa tsoro mai tsanani a cikin zukatan kafirai, inda suka ja baya, bayan sun kudiri aniyar yin kisan gilla a kan muslmi a cikin birnin Madina. Sai wannan ayar ta safka, domin yaba wa musulmi da kuma jaruntar da suka nuna.
Wannan ayar tana koyar da mu wani babba darasi, shi ne cewa idan musulmi suka san abin da ya rataya kansu kuma suka yi aiki da umurnin Allah, to za su samu taimakon ubangiji a cikin dukkanin halin da suka samu kansu na tsanani. 919668
captcha