IQNA

Tawagar Kiristocin Kasar Lebanon Ta Gana Da Sayyid Hassan Nasrullah

14:50 - December 21, 2011
Lambar Labari: 2242931
Bangaren kasa da kasa, wata tawagar mabiya addinin kirista a kasar Lebanon da shugaban kiristocin kasar ya aike zuwa ga Sayyid Hassan Nasrullah, sun gana da shi kuma sun bayyana matukar gamsuwa dangane da yadda ya karbe da kuma yadda yake girmama jagoransu.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-manar cewa, tawagar mabiya addinin kirista a kasar Lebanon da shugaban kiristocin kasar ya aike zuwa ga Sayyid Hassan Nasrullah, sun gana da shi kuma sun bayyana matukar gamsuwa dangane da yadda ya karbe da kuma yadda yake girmama jagoransu Batriyak Al-rai.
Wanda ya jagoranci tawagar ya bayyana cewa irin matakin Sayyid Nasrullah ya dauka tun bayan zaben shugaban nasu abun yabawa ne matuka, domin kuwa a matsayinsa na babban mutum da yake da dimbin magoya baya a kasar Lebanon ya fito karara ya nuna goyon bayansa ga shugaban kiristocin kan aniyarsa ta kira ga zamn lafiya da hada kan al’ummar kasar.
Wannan tawagar mabiya addinin kirista a kasar Lebanon da shugaban kiristocin kasar ya aike zuwa ga Sayyid Hassan Nasrullah, bayan ganawa da shi kuma sun bayyana matukar jin dadi kan kyakyawar fahimta da ke akwai tsakanin mafi yawan kiristocin Lebanon da kuma kungiyar Hizbullah.
919451

captcha