Kmafanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa ya naklato daga shafin sadrawa na yanar giz na isvt cewa, ana shirin gudanar da wata gasar hardar kur’ai mai tsarki a birnin Warmont na kasar Amurka wadda za ta kebanci kanan yara ‘yan makaranta musulmi mazauna birnin, wanda babbar cibiyar kula da harkokin muslunci ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Wannan gasa za ta ha bangarori daban-daban na kur’ani, da suka hada da hardar bangare na farko na kur’ani mai tsarki, da kuma bangare na biyu wato daga farko zuwa tsakiya, sai kuma wadanda za su kammala kur’ani baki daya acikin gasar, duk kuwa da cewa akwai sauran lokaci da ya kai kimani watanni uku kafin gudanar da ita.
Yanzu haka dai ana shirin gudanar da wata gasar hardar kur’ai mai tsarki a birnin Warmont na kasar Amurka wadda za ta kebanci kanan yara ‘yan makaranta musulmi mazauna birnin Warmont.
Musulmin kasar Amurka suna yin matukar kokari wajen ganin sun sun kiyaye lamurra na addininsu, duk kuwa da irin tsangwamar da ake yi musu saboda addininsu, wanda kuma haka ba ya rasa nasaba da kiyaya da musulunci yahudawan sahyuniya suke yi.
919385