Bangaren kasa da kasa; a karo na arba'in an fara gudanar da taron komitin tattalin arziki na kungiyar hadin kan kasashen musulun a ranar ashirin da takwas ga watan azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a hedkwatar kungiyar da ke birnin Jidda fadar mulkin kasar Saudiya.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa : a karo na arba'in an fara gudanar da taron komitin tattalin arziki na kungiyar hadin kan kasashen musulun a ranar ashirin da takwas ga watan azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a hedkwatar kungiyar da ke birnin Jidda fadar mulkin kasar Saudiya.A cikin wannan taro da za a kwashe kwanaki uku ana gudanarwa mukaddashan ministocin kudadai na kasashe mambobi a cikin kungiyar ta hadin kan kasashen musulmi za su tattaunawa da binciken hanyoyin binkasa tattalin arziki da kasuwanci da ajiyar kudai a cikin kasashensu da kuma hanyoyin da za su bi wajan magance irin matsalolin tattalin arziki da kasashen kungiyar ta hadin kan kasashen musulmi ke fuskanta .Har ila yau Ikmalul Dine Uglo babban sakataren kungiyar ta hadin kan kasashen musulmi ya gabatar da jawabin bude wannan taro inda a cikin jawabinsa ya yi bayani kan nauyin da kasashen kungiyar suka daura masu na samara da hanyoyin da za a bi wajan habaka tattalin arziki da kasuwanci a tsakanin kasashen da kuma a tsakaninsu da sauran kasashen duniya.
919272