IQNA

Babban Muftin Kudus Ya Yi Allah Wadai Da Harin Da Yahudawa Suka Kai Kan Masallacin Kudus

Bangaren kasa da kasa: babban muftin birnin kudus a cikin wani bayani day a aikewa shugabannin gwamnatin yahudawan sahayoniya ya yi Allah wadai da kaukausar murya kan harin da mamaye masallacin Kudus Mai tsarki da wasub yahudawan sahayoniya yan share guri zauna suka yi da kuma a cikin wasikar ya shaida masu bacin ran musulmin duniya kan wannan danyan aiki.

Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; babban muftin birnin kudus a cikin wani bayani day a aikewa shugabannin gwamnatin yahudawan sahayoniya ya yi Allah wadai da kaukausar murya kan harin da mamaye masallacin Kudus Mai tsarki da wasub yahudawan sahayoniya yan share guri zauna suka yi da kuma a cikin wasikar ya shaida masu bacin ran musulmin duniya kan wannan danyan aiki.Sheikh Muhammad Husein babban mai fitar da fatawa a birnin Kudus ya kara da cewa wasu yahuwa yan share guri zauna ne suka kai hari na mamaye da nuna karfi da dabbanci lamarin day a bakantawa musulmin yankin da rai har ila yau muftin ya yi nuni da yawaitar kai hare hare da mamaye kan masallacin kudus mai tsarki da guraren ibada na musulmi da na kiristoci a yankin da sauran kauyuka da ke yankin da cewa wannan kaita hurumin guraren ibada abin kama ne da babu wani musulmi ko kirista da zai yarda da hakan.

920789