IQNA

Ana Ci Baga Da Gudanar Da Zanga _zangar Kin Masarautar Ali Saudiya A Awamiya

13:14 - December 24, 2011
Lambar Labari: 2244084
Bangaren kasa da kasa;a garin Awamiya na kasar Saudiya ana ci gaba da gudanar da zanga-zangar ganin sai an hukumta masu hannu a kisan gillar da aka yi wa wasu matsa yan kasar ta Saudiya su hudu a cikin watan da ya gabata.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a garin Awamiya na kasar Saudiya ana ci gaba da gudanar da zanga-zangar ganin sai an hukumta masu hannu a kisan gillar da aka yi wa wasu matsa yan kasar ta Saudiya su hudu a cikin watan da ya gabata.Su dai wadannan matasa hudu yan kasar ta saudiya a cikin watan da ya gabata ne a lokacin gudanar da wata zanga-zangar lumana ta neman kawo sauyi da sausauci ga lamuran kasar a gabacin Saudiya jami'an tsaro suka bude masu wuta da bindige su har lahira inda suka yi shahada .wadanda suka gudanar da zanga-zangar suna bukatar a hukumar jami'an tsaro na gwamnatin Saudiya da suka bude wuta da bakin bindiga har wadannan matasa hudu suka yi shahada kuma wadanda suka gudanar da wannan zanga-zangar suna dauke da hotunan wadannan matasa hudu tare da bukatar Muhammad Bin Fahad hakimin yankin Alsharkiya ta Saudiya.

920786


captcha