Kamfanin dillancin labaran iqna ya habrta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na felesten cewa, Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta sanar cewa a gobe majalisar Keneset za ta kada kuri'a kan wani daftarin doka da ke nufin amincewa da birin Qods a matsayin fadar mulkin gwamnatin yahudawan sahyuniya a hukumance.
Wannan daftarin doka dai yana mayar da birnin Qods fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra'ila, tare da mayar da dukkanin harkokin siyasa da diplomasiyarta a birnin, da kuma mayar da palastinawa da suke cikin birnin saniyar ware. Tun a cikin watan Yulin shekara ta 1980 ne haramtacciyar kasar Isra'ila ta shelanta birnin Qods a matsayin babban birninta, amma amincewar majalisar Kenesent da daftarin doka zai mayar da birnin na Qods fadar mulkin gwamnatin yahudawan sahyuniya a hukumance.
A cikin wannan makon ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta amince da wani shiri na gina matsugunnan yahudawa 60,000 a cikin yankunan palastinawa da ke gabacin birnin Qods, lamarin da ya fuskanci kakkausar suka daga kasashen duniya daban-daban da suka hada har da na yammacin turai, amma Amurka taki amincewa da rashin halascin hakan, maimakon hakan ma ta hau kujerar naki a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya a lokacin da dukkanin mambobin kwamitin suka amince da daftarin kudiri da ke yin Allawadai da HKIsra'ila kan mamayar yankunan palastinawa.
921504