IQNA

Addinin Musulunci Na Samun Karbuwa A Cikin Kasashen Turai

19:22 - December 25, 2011
Lambar Labari: 2245018
Bangaren kasa da kasa, addinin muslunci yana samun matukar karbuwa acikin sauri a tsakanin al’ummomin yankin nahiyar turai wanda hakan ke nuni da cewa daga nan zuwa karshen karnin da muke ciki addinin zai zama addini na farko a cikin nahiyar turai.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, jaridar Yadiut Ahrunut ta yi ishara da cewa, addinin muslunci yana samun matukar karbuwa acikin sauri a tsakanin al’ummomin yankin nahiyar turai wanda hakan ke nuni da cewa daga nan zuwa karshen karnin da muke ciki addinin zai zama addini na farko a cikin nahiyar turai wadda a halin yanzu ake nuna ma musulmi kyama a cikinta.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan karbuwa da musulunci yake samu ba ta rasa nasaba da wasu daga cikin abubuwan da ake dangatawa da musuluncin ne, domin kuwa yadda kasashen turai suke nuna adawa ga addinin musulunci ko shakka babu hakan zai yi tasiri a cikin zukatan wasu, da zai sanya su bincike kan wannan addini, kuma daga karshe za su karbe shi.

Wasu manazarta suna ganain cewa addinin muslunci yana samun matukar karbuwa acikin sauri a tsakanin al’ummomin yankin nahiyar turai wanda hakan ke nuni da cewa daga nan zuwa karshen karnin da muke ciki addinin zai zama addini na farko a cikin nahiyar turai da ma wasu yankuna na nahiyar Asia.

921386
captcha