IQNA

Bincike Kan Muhimmancin Muhimmancin Iyali A Musulunci

Bangaren al'adu fasaha:an fara wani bincike da za a kwashe mako guda cir ana gudanarwa a garin Cubuk na kasar Turkiya inda masana za su yi kan muhimmancin gina iyali a mahangar musulunci da kuma koyarwar limaman masalatai na Turkiya.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; an fara wani bincike da za a kwashe mako guda cir ana gudanarwa a garin Cubuk na kasar Turkiya inda masana za su yi kan muhimmancin gina iyali a mahangar musulunci da kuma koyarwar limaman masalatai na Turkiya.A cikin wadannan makonni da za har guda takwas za su tattauna da bincike kan abubuwa da dama kamar dangataka tsakanin iyali da kira zuwa ga sulhu da kwanciyar hankali da yadda za a tunkari matsala don magance ta ,aure da abun da ak bukata daga bangarorin biyu ,rawar da uba da uwa ke takawa da sauran dokoki da suka danganci iyalai da gina iyalan da dokokin zamantakewa da muhimmancin mata a musulunci na daga cikin abubuwa da za a tattaunawa wannan bincike.




922951