IQNA

Ma'aikatar Shari'a Ta Hamas Ta Damu da Gum Da Kasashen Duniya Suka Yi

15:37 - December 27, 2011
Lambar Labari: 2246443
Bangaren kasa da kasa; ma'aikatar shari'a karkashin zabebbiyar gwamnati a Palsdinu da ke mulki yankin Gaza ta fitar da wani bayani da a cikinsa take mayar da martini kan daftarin doka da Haramtacciyar kasar Isra'ila take shirin kaddamarwa don amfanin yahudawa yan share guri zauna da bayyana rashin jin dadi da damuwa kan shiru da gum da baki da kungiyoyi da hukumomi na kasa da kasa da sauran kasashen duniya da na yankin suka yi kan wannan matakin nua wariya na gina matsugunnan yahudawa.




Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; ma'aikatar shari'a karkashin zabebbiyar gwamnati a Palsdinu da ke mulki yankin Gaza ta fitar da wani bayani da a cikinsa take mayar da martini kan daftarin doka da Haramtacciyar kasar Isra'ila take shirin kaddamarwa don amfanin yahudawa yan share guri zauna da bayyana rashin jin dadi da damuwa kan shiru da gum da baki da kungiyoyi da hukumomi na kasa da kasa da sauran kasashen duniya da na yankin suka yi kan wannan matakin nua wariya na gina matsugunnan yahudawa. Wani mataki da kokarin takalar fada gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila na shirin kaddamar da wani daftarin dauka na mayar da birnin Kudus mai tsarki fadar mulkin yahudawa da hakan a fili karara ke nuni da mamaye Palasdinu da take daokokin kasa da kasa amma abin mamaki da takaici yadda kasashen duniya da hukumomi da kungiyoyi na kasa da aksa da uba uba na yankin suka yi gum bas u cewa komi kan wannan matsala a cikin wannan lamari mai daurin kai.

923033
captcha