IQNA

Sheikhul Azhar Ya Ce Kare Masallacin Qods Wajibi Ne Kan Al’ummar Musulmi

16:51 - December 27, 2011
Lambar Labari: 2246480
Bangaren kasa da kasa, babban malamin jami’ar Azhar kuma mai bayar da fatawa sheikh Ahmad Tayyib ya bayyana cewa wajibi ne da ya rataya kan al’ummar musulmi su kare masallacin Qods mai alfarma da dukkanin karfin da Alla ya huwace musu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na CPI cewa, babban malamin jami’ar Azhar kuma mai bayar da fatawa sheikh Ahmad Tayyib ya bayyana cewa wajibi ne da ya rataya kan al’ummar musulmi su kare masallacin Qods mai alfarma da dukkanin karfin da Alla ya huwace musu bisa la’akari da yunkurin yahudawan sahyuniya dake barazana ga wannan masallaci da sauran wurare masu alfarma a birnin.
Kwamitin hadin gwiwa na musulmi da kiristoci a yankin palastinu ya yi kakkausar da yin Allawadai da yunkurin haramtacciyar kasar Isra’ila na mayar da birnin Qods mai alfarma fadar mulkinta, tare da kiran dukaknin mulmi da kiristoci da sauran mutanen duniya masu lamiri, da su taka wa wannan makrci birki cikin gaggawa.
Malamin jami’ar Azhar kuma mai bayar da fatawa sheikh Ahmad Tayyib ya bayyana cewa wajibi ne da ya rataya kan al’ummar musulmi su kare masallacin Qods mai alfarma da dukkanin karfin da Alla ya huwace musu, domin yin shiru kan hakan babban laifi ne da Allah zai kama al’ummar musulmi kansa.
922690


captcha