IQNA

Majalisar Musulmin Kasar Birtaniya Sun Yi Allawadai Da Harin Bam A Nigeria

12:58 - December 28, 2011
Lambar Labari: 2247034
Bangaren kasa da kasa, musulmin kasar Birtaniya sun yi Allawadai da kai harin bam da aka yi a Nigeria akan masu gudanar da tarukan kirsimiti a kusa birnin Abuja fadar mulkin kasar.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Arabic.upi.com cewa, mabiya adddinin Musulunci a kasar Birtaniya sun yi Allawadai da kai harin bam da aka yi a Nigeria akan masu gudanar da tarukan kirsimiti a kusa birnin Abuja fadar mulkin kasar day a yi sanadiyar mutuwar mutane sama da talatin.

A nasa bangare tsohon shugaban kasar Nigeria Janar Muhammad Buhari ya ce rashin shuwagabanni na korai wadanda zai tunkari matsalolin kasar ne ya sa harkokin tsaro suke kara tabarbarewa a kasar.
Buhari ya fadawa wata jaridar kasar cewa gwamnatin kasar tana tafiyar hawainiya a wajen tunkarar matsalolin tsaron kasar. Ta yaya, injishi fadar Vatikan da kuma gwamnatin kasar Britania zasu rika gwamnatin kasar Magana a kan wani abu da ya faru ga yan kasar ta Nigeria a kuma cikin kasar.
Tsohon shugaban kasar ya kara da cewa gwamnatin kasar tana bukatar yin aiki da gaske kan harkokin samara da tsaro fiye da kara yawan kudaden da zata kasha a harkokin tsaro.

A jiya lahadi ne dai, kuma ranar kirsimeti, wasu boma bomai suka tashi a cikin chuchi chichi guda ukku a kasar, wanda ya halaka mutane kimani 40 ya kuma raunata wasu da dama.
Kamfanin dillancin labarum reutera ya ce jami'an tsaron kasar Nigeria sun zargi kungiyan nan da ake kira Boko Haram da kai hare hare a wasu wurare biyu a arewacin kasar a jiyan.
923664

captcha