IQNA

Za A Kaddamar Da Talbijin Ta farko Ta mUsulunci A Tunusiya

Bangaren kasa da kasa: a karon farko a kasar Tunusiya za a kaddamar da talbijin ta farko ta musulunci da za ta rika gabatar da shirye-shiryenta ta hanyar tauraron dan adam kuma wannan talbijin da za ta rika watsa shirye-shiryen nata daga garin Safakas an bata sunan Alkalam.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a karon farko a kasar Tunusiya za a kaddamar da talbijin ta farko ta musulunci da za ta rika gabatar da shirye-shiryenta ta hanyar tauraron dan adam kuma wannan talbijin da za ta rika watsa shirye-shiryen nata daga garin Safakas an bata sunan Alkalam.Tun bayan kifar da gwamnatin bin Ali a kasar Tunusiya aka fara samin yancin gudanar da ayyukan addinin musulunci a wannan kasa kuma a kan wannan dalili ne hadin guiwar limaman garin Safakas suka yi niyar kafa talbijin ta farko ta musulunci da za ta rika watsa shirye-shiryenta ta hanyar tauraron dan adam.


923506