IQNA

An Kaita Hurumin Makabartar Musulmi A Kuduncin Faransa

17:22 - December 28, 2011
Lambar Labari: 2247283
Bangaren kasa da kasa: kimanin makwanciyar sojoji musulmi talatin ne da suka yi yakin duniya na farko a ranar biyar ga watan Dai na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in a kasar Faransa wasu masu bakar nuna adawa da banbanci kan musulmi da musulunci suka kai masu hari.

Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: kimanin makwanciyar sojoji musulmi talatin ne da suka yi yakin duniya na farko a ranar biyar ga watan Dai na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in a kasar Faransa wasu masu bakar nuna adawa da banbanci kan musulmi da musulunci suka kai masu hari.Wannan shi ne karo na biyu a cikin yan watannin baya bayan nana ka kai wa makabartar San Mishel daga garin Carcassonne a kuduncin kasar faransa harin nuna wariya da banbancin addini. Wadanda suka kai wannan hari bayan sun tona kabarin musulmi sun kuma yi rubuce-rubucen cewa dole musulmi su fice daga kasar Faransa ,faransa ta faransawa ce da kuma rubuta alamar kiristanci a kan kaburburan da suka lalata.


923495

captcha