Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto dagashafin sadarwa na yanar gizo ma OIC cewa, kungiyar kasashen musulmi ta yi kakkausar da yin Allawadai kan yunkurin yahudawan sahyumiya na neman mayar da birnin Qods fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra'ila kuma babban birnin Yahudawa na duniya baki daya.
A bangare guda kuma wasu rahotannin sun ce wani bapalastine guda ya yi shada wasu goma sha daya kuma sun samu raunuka, sakamakon hare-haren da jiragen yakin Haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai yankin Zirin Gaza.
Mai'ako ma gidan talabijin dil Al-alam rahotanni daga Zirin Gaza ya ce, jiragen yakin yahudawan sahyuniya sun harba makamai amasu linzami a yankin Jabaliyya da ke cikin zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadiyar shahadar wani matashi mai suna Abdullah Talbani da n shekaru 22 da haihuwa, tare da jikkata wasu palastina a kalla 11.
Wadannan hare-hare dai sun zo ne a lokacin palastinawa suke tarukan cika shekaru da haramtacciyar kasar Isra'ila ta kaddamar da yaki kan al'ummar palastinawa mazauna zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadiyar yin shahadar palastinawa akalla 1400, wasu sama da dubu biyar kuma suka samu raunuka.
Wasu daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa sun zargi Isra'ila da aikata laifukan yaki a Gaza, haka nan kuma kungiyoyin sun zargi Amurka da wasu daga cikin kasashen larabawa da taimaka ma gwamnatin yahudawan a lokacin yakin Gaza.
923552