Bangaren kasa da kasa; cibiyar kwararru kan harkokin kudi a musulunci Albiyan a watan farverdin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya za ta gudanar da taronta na kasa da kasa kan harkokin kudi a tsarin musulunci karo na hudu a birnin khartum fadar mulkin kasar Sudan.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: cibiyar kwararru kan harkokin kudi a musulunci Albiyan a watan farverdin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya za ta gudanar da taronta na kasa da kasa kan harkokin kudi a tsarin musulunci karo na hudu a birnin khartum fadar mulkin kasar Sudan. A wannan taron na tsarin kudi na musulunci za a samu halartar mu'assishin kudi da bankokin musulunci CBAFI da asusun ajiyar na Khartum da kuma mua'ssisar kasa da kasa ta Basant inda a lokacin wannan taro za su tattaunawa da bayani kan irin hanyoyin da za su bi domin inganta harkokin kudi da tattalin arziki a kasashen musulmi da kula irin kalubanlan da suke fuskanta da matsalolin da suka fusknata a baya domin magance su.Kuma kimanin mu'asishin kudi a tsari irin na musulunci kimanin hamsin ne daga kasashen Saudiya'bahrain,Hadeddiyar daular larabawa da Jodan ,Malaishiya,Faransa,Britaniya,Turkiya da kuma wasu kasashen musulmi za su halarci wannan taron.
924743