Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na AllAfrica cewa, a ranar laraba da ta gaba ne wani bam da aka dana acikin wata makarantar kur’ani a yankin Niger Delta da ke kudancin tarayyar Nigeria ya tarwatse kuma ya yi sanadiyyar jkikkatar wasu daga cikin daliban makarantar a wani mataki da ake ganin ya yi kam ada na daukar fansa kan mabiya addinin muslunci da suke zaune a wannan yanki, wanda akasarin mazaunansa mabiya addinin kirista ne.
Rahoton bayan kai harin a nan take dai yara bakwai ne daga cikin masu karatun kur’ani wannan makaranta suka samu raunuka, kuma a nan take a ka dauke su zuwa asibiti domin yi musu maganai, haka nan kuma makonni biyu kafin wannan lokacin ma wani bam din ya tashi a cikin wani masallaci da ke yankin, wanda shi ma ya yi sanadiyar lalacewar wasu ababuwan masallacin.
Bam din da aka dana a cikin makarantar kur’anin a yankin Niger Delta da ke kudancin tarayyar Nigeria wata manuniya ce ta rashin tsaro a Nigeria, kuma hakan yana yin ishara da cewa akwai rikici a kasar matukar dai mahukunta ba su dauki matakan da suka dace ba.
925529