Bangaren kasa da kasa, an buga tare da yada wani sabon kwafin kur’ani mai tsarki da aka tarjama acikin harshen turancin Ingilishi a kasar Masar, wanda mu’assar nan ta yada alittafan muslunci ta Dar Al-shuruk ta dauki nauyin bugawa da yadawa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna yahabarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanr gizo na Al-shuruk cewa, an buga tare da yada wani sabon kwafin kur’ani mai tsarki da aka tarjama acikin harshen turancin Ingilishi a kasar Masar, wanda mu’assar nan ta yada alittafan muslunci ta Dar Al-shuruk ta dauki nauyin bugawa da yadawa a cikin wannan mako.
A bangare guda kuma dubban mutane a yankin sayyidah Zainab da ke cikin birnin Alkahira na kasar Masar sun yi cincirindo kan titunan yankin domin nuna rashin amincewa da hukuncin da kotun kasar ta yanke na sallamar mutaen da suke da hannu a kisan da aka yi wa masu boren da aka yi a kasar wanda ya kawo karshen mulkin kama karya na tsaohon shugaban kasar.
Wadanda suka yi zanga-zangar sun yi ta rera taken kalmar shahada tare da nemana yi hukunci na gaskiya da adalci kan mutanen mubarak da suka kashe mutane a lokacin juyin juya halin kasar, domin kuwa mutaen dukkansu ana zargin da hannu dumu-dumu a wannan tabargaza da ta afku a kasar ta Masar.
925510