Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Paletine cewa, limamin masallacin Qods mai alfarma sheikh Ikrama ya yi kakkausar suka kan samamen da sojojin yahudawan sahyuniya suke kaiwa kan al'ummar palastinu mazauna birnin mai alfarma a cikin 'yan kwanakin nan.
A wani labarin kuma Wani bapalastine ya yi shahada sakamakon harba makamai masu linzami da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila suka yi a yankin zirin Gaza.
Kakakin ma'aikatar kiwon lafiya a yankin zirin Gaza Ashraf Kudra ne ya sanar da hakan a yau, inda ya ce jiragen yakin haramtacciyar gwamnatin yahudawan sahyuniya sun kaddamar da harin ne kan al'ummar palastinu mazauna yankin Hajr Dik da ke gabacin zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadiyar yin shahadar matashi bapalastine mai suna Mu'umin Abu Daf tare da jikkatar wasu.
Kimanin shekaru uku da suka gabata a daidai irin wannan lokacin ne haramtacciyar kasar Isra'ila tare da taimakon Amurka, da kuma hadin baki da wasu daga cikin kasashen larabawa, ta kaddamar da harin soji kan al'ummar musulmi mazauna yankin zirin Gaza, lamarin day a yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 1400, akasarinsu kanan yara ne da mata.
925961