Bangaren kasa da kasa: Ayatullahi Uzma Bashir Najafi marja'in addini na yan shi'ar Iraki ya bukaci yan mamaya su bar kasar ta shakata ta fuskar mulkin mallaka na tunani ,al'adu,tattalin arziki, Siyasa,Tsaro da kuma uwa uba zamantakewa.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Ayatullahi Uzma Bashir Najafi marja'in addini na yan shi'ar Iraki ya bukaci yan mamaya su bar kasar ta shakata ta fuskar mulkin mallaka na tunani ,al'adu,tattalin arziki, Siyasa,Tsaro da kuma uwa uba zamantakewa.Ayatullahi Bashir Najafi ya fadi haka ne a lokacin wani jawabinsa da Ali Najafi danasa ya karanto a madadinsa a taron murnar ficewa sojojin mamaya na Amerika daga Iraki da aka shirya a birnin Najaf da cewa: muna yin godia ga Allah madaukakin sarki da ya yaye mana wannan kunci da bakin cikin kasancewar sojojin mamaya a kasarmu .Kuma wata babbar nasara ce da fita daga kaskanci na kasancewar sojojin mamaya a cikin kasarmu:Sojojin mamaya na kasar Amerika a karshen watan jiya na desamba shekara ta dubu biyu da goma sha daya suka fice daga kasar Iraki.
926581