IQNA

Al'ummar Yankin Sun Baranta Da Gwamnatocin Yankin

Bangaren kasa da kasa: Imamin juma'a na yankin yan shi'a a Alawamiya na kasar Saudiya ya bayyana cewa; al'ummomin yankin sun yi hannun riga da baranta da gwamnatoci da mahukumtan yankin kuma suna da hakkin nisantan masu yin mulki a kasashen yankin.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Imamin juma'a na yankin yan shi'a a Alawamiya na kasar Saudiya ya bayyana cewa; al'ummomin yankin sun yi hannun riga da baranta da gwamnatoci da mahukumtan yankin kuma suna da hakkin nisantan masu yin mulki a kasashen yankin.Ayatullahi Sheikh namr Bakir Alnamr a hudubar day a gabatar a lokacin sallar juma'ar da ta gabata a ranar tara ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya bayana takaicinsa da hare haren mamaya da sojojin da jami'an tsaro na Saudiya ke kaiwa mazauna yankin tare da yin Allah wadai kuma ya bayyana cewa mahukuma da gwamnatocin yankin sun yi hannun rika da nisantar mutanan yankin kuma mahukumtan babu wata mazhaba ta musulunci da ke bi kawai abin day a damai su kare mulkinsu da yadda za su ci gaba da zama kan karagar mulki da mulkar mutanansu.


926511