IQNA

Baje Kolin Kasa Da Kasa Karo Na Farko Na Marubuta Mata Musulmi

14:29 - January 02, 2012
Lambar Labari: 2249885
Bangaren al'adu da fasaha; a karon farko za a gudanar da kasuwar baje kolin kasa da kasa ta marubuta mata musulmi daga ranar sha bakwai ga watan Dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya zuwa a shirin da biyu ga watan na Dai a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar musulunci ta Iran kuma ofishin da a ke kula da harkokin mata da iyali na hukumar kula da al'adu da dangantaka ta musulunci ne ya shirya.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a karon farko za a gudanar da kasuwar baje kolin kasa da kasa ta marubuta mata musulmi daga ranar sha bakwai ga watan Dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya zuwa a shirin da biyu ga watan na Dai a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar musulunci ta Iran kuma ofishin da a ke kula da harkokin mata da iyali na hukumar kula da al'adu da dangantaka ta musulunci ne ya shirya. Har ila yau kimanin marubuta ashirin da bakwai ne daga kasashen waje da suka hada daga kasashen Asiya ,Afrika da Turai da kuma marubuta na cikin gida za su halarci wannan taro na marubuta mata musulmi da za a yi a nan birnin Tehran.A lokacin gudanar da wanann taron matan za su tattauna a tsakanin da yin nazarin hanyoyin fadada wannan bangare na rubutu da kuma tattauna matsalolin da suke fuskanta domin yin dubi a cikin shawawarwarin hanyoyin magance irin matsalolin da suke fuskanta a kasashensu da kuma hada karfe da karfe guri guda a tsakaninsu domin fadadawa da ciyar da wannan manufa gaba.


926662

captcha