IQNA

A Rubuce Musulmin Tailand Sun Nuna Adawa Da Hana Sanya Hijabi A Makarantu

Bangaren siyasa da zamnatakewa; musulmin kasar tailand a rubuce sun nuna adawa da kalubalantar matakan da wasu makarantun kasar ke dauka na hana wa mata yara kanana sanya hijabi ko takura masu a cibiyoyin ilimi da koyarwa na kasar.


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: musulmin kasar tailand a rubuce sun nuna adawa da kalubalantar matakan da wasu makarantun kasar ke dauka na hana wa mata yara kanana sanya hijabi ko takura masu a cibiyoyin ilimi da koyarwa na kasar.Wani adadi ne na musulmi day an jami'a musulmi a wannan kasa ta Tailand a ranar tara ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a cikin wata wasika da suka rubuta suke sukan wasu makarantu da cibiyoyin ilimi da ke hana yan mata kanana masu sanye da hijabi shiga makarantunsu domin daukan ilimi da cewa wannan mataki ne day a sabawa dokokin ilimi da zamantakewar kasar kuma dole ne a yi bincike da kawo karshen wannan lamari na nuna wariya .Wannan mataki da wasu makarantun ke dauka wani nauyi ne na take hakkin dan adam a kasar da kuma ba za su taba yarda da daukan raini ba kan hakan.


926769