IQNA

Palastinu Za Ta Kai Karar Haramtacciyar Kasar Isra’ila A Kwamitin Tsaro

17:41 - January 02, 2012
Lambar Labari: 2250016
Bangaren kasa da kasa, mahukunta a palastinu sun sha alwashin kai karar haramtacciyar kasar Isra’ila a gaban kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya saboda ci gaba da mamayr yankunan palastinawa da take yi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dilalncin labaran KUNA na kasar Kuwait cewa, mahukunta a palastinu sun sha alwashin kai karar haramtacciyar kasar Isra’ila a gaban kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya saboda ci gaba da mamayr yankunan palastinawa da take yia halin yanzu a yankunan gabacin birnin Qods.
A wani labarin kuma hukumomi a kasar Palasdinu sun bayyana cewa HKI ta kashe Palasdinawa 180 a cikin shekarar da ta gabata ta 2011, gidan television na PressTv ya nakalto wani rahoto wanda da kungiyar kwatar 'yencin Palasdinawa ta PLO ta fitar a yau Lahadi yana cewa 120 daga cikin wadanda sojojin HKI ta kashe sun hada da mata da kuma yara kananan. Sannan wasu 600 kuma suka ji rauni.
Rahoton ya kara da cewa shekara ta 2011 ita she shekara mafi muni ga Palastinawa tun bayan yakin Gaza, Ashraf Al-qedra wani jami'in lafiya a asbitin Gaza ya bayyana cewa har yanzun asbitin gaza yana fama da karancin wasu magunguna masu muhimmanci.
Tun shekara 2007 ne Hki ta killace yankin Gaza ta sama, kasa da kuma ruwa wanda ya maida yankin gidan yari mafi girma a duniya. Kimanin Palasdinawa miliyon daya da rabi ne suke rayuwa a yankin na gaza.
926702

captcha