IQNA

Komitin Musulmin Faransa Sun Bukaci Al'ummar Kasar Da Su Hada Kai

15:39 - January 03, 2012
Lambar Labari: 2250686
Bangaren kasa da kasa: komitin musulmin Faransa ta CFCM a ranar sha daya ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya sun fitar da wani bayani da a cikinsa suka bukaci al'ummar kasar ta Faransa da su hada kai da fahimtar juna da girmama juna.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: komitin musulmin Faransa ta CFCM a ranar sha daya ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya sun fitar da wani bayani da a cikinsa suka bukaci al'ummar kasar ta Faransa da su hada kai da fahimtar juna da girmama juna.Muhammad Musawi shugaban komitin musulmin kasar Faransa a wani sakon taya murnar shiga sabuwar shekara ta dubu biyu da goma sha biyu zuwa gay an kasar ta Faransa yayi fatar wannan shekara ta kasance shekara mai albarka da alheri da kuma ta kasance shekarar hadin kai da fahimtar juna a tsakanin yan kasar ta Faransa da kuma ci gaba ta fuskar addini da kusanci na zamantakewa da kawo karshen irin wariya da banbance banbance da ake nunawa musulmin kasar ta faransa . A wani bangare na jawabin nasa ya kuma yi fatar wannan matsalar tattalin arziki da ake fuskanta ya kawo karshe da daidaita a duniya.


927287

captcha