IQNA

An Watsa Wata Kalanda Ta Hadin Guiwa Tsakanin Musulunci Da Kiristanci

Bangaren kasa da kasa: wasu gungun musulmi na kasar Faransa da kuma takwarorinsu kiristocin kasar ta Faransa sun hada kai da fitar da kalandar ta hadin guiwa da ta hada kwanan wata na miladiya da kamariya.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: wasu gungun musulmi na kasar Faransa da kuma takwarorinsu kiristocin kasar ta Faransa sun hada kai da fitar da kalandar ta hadin guiwa da ta hada kwanan wata na miladiya da kamariya.Shugabannin cocin garin Albi tare da hadin guiwar hadin kungiyoyin Musulunci na Muhibbani Islami a wannan gari a karo na hudu a cikin shekaru a jeer suna rubuta kalanda da ta hada kwanan wata na kiristanci da na Musulunci misali shekara ta dubu biyu da goma sha biyu miladiya da shekara ta dubu daya da dari hudu da talatin da uku hijira kamariya.Wannan matakin na jinjinawa da kuma ke isar da sakon kara samun hadin kai a tsakanin mabiya addinan guda biyu na musulmi da kuma na kiristanci musamman a daidai wannan lokacin da masu kulla makirci ke kara kullawa mabiya addinai guda biyu makirci su kara hada kansu domin dakilai da maida makiyansu mummunan aniyarsu.


927216