Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan ana gudanar da taron kasa da kasa kan Kudus mai taken hadarin da ke tattare da guna matsugunnan yahudawa yan share guri zauna a Kudus.Wannan taron ana gudanar da shi tare da halartar manyan jami'ai na hukuma a kasar ta Sudan da na Palasdinu da kuma wakilan kungiyoyin kasa da kasa da na yankin daga cikin manyan baki da suka halarci wannan taro akwai Isma'ila Haniya shugaban gwamnatin Hamsa kuma zabebben firaministan Palasdinu da kuma Nafi'I Ali Nafi'I mukaddashin farko na shugaban kasar Sudan da Kutubi Almahdi shugaban muassisar kasa da kasa ta kudus bangaren Sudan da Akbali da dai sauran manyan baki da jami'ai na duniyar musulmi .Har ila yau an gabatar da jawabai masu gamsarwa a gurin wannan taro mai matukar muhimmanci dad au hankalin jama'a adaidai wannan lokaci da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kullawa musulmi da Palasdinawa makirci da ci gaba da siyasar gina matsugunnan yahudawan sahayoniya yan share guri zauna.
927415