IQNA

Zaman Taron manema Labarai Na Baje Kolin Kasa Da Kasa Na Labaran Matan Musulmi

Bangaren al'adu da fasaha; Sadika Hijazi babba sakatariyar shirya kasuwar baje kolin ta gabatar da taron manema labarai kan samara da kafar labarai ta mata musulmi .



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Sadika Hijazi babba sakatariyar shirya kasuwar baje kolin ta gabatar da taron manema labarai kan samara da kafar labarai ta mata musulmi .A yau sha uku ga watan Dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a ofishin mukaddashin al'adu a hukumar kula da al'adu da dangantaka ta Musulunci aka gudanar da taron manema labarai na kasuwar kasa da kasa ta kafa kafar labarai na mata musulmi da aka bawa taken mata da kafafen watsa labarai da kuma irin rawar da za su taka a wannan bangare. Wannan taroo dai an fara shi ne tare da jawabin Sadika Hijazi da ta gabatar da jawabi mai gamsarwa da kuma kayatarwa da kuma bayani dalla dalla kan muhimmancin bawa mata damar taka rawar da za su iya a wannan bangare na labarai da kafafen watsa labarai kuma yin hakan zai taimaka wajan habaka harkar labarai a duniyar musulmi.

928349