Bangaren siyasa da zamantakewa; an gudanar da bukin kamala gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka gudanar a garin Tenenku a laradin Mapati kuma hadin guiwar kungiyar yan jami'a musulmi a kasar ne ya shirya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: an gudanar da bukin kamala gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka gudanar a garin Tenenku a laradin Mapati kuma hadin guiwar kungiyar yan jami'a musulmi a kasar ne ya shirya.Wannan bukin rufe wannan gasar karatun kur'ani mai tsarki a kasar ta mali an gudanar tare da halartar Sheikh Mahmud Diko shugaban majalisar koli ta musulmin wannan kasar ta Mali da ke yammacin nahiyar Afrika da kuma Saidu Tumani Kamara gwamnan lardin Maubati da kuma wasu daga cikin mashawarta da magadanyan garuruwan yankin. A wannan gasar kimanin makaranta kur'ani yan kararanta dari ne suka halarta da kuma suka fito daga yankuna daban daban na kasar ta Mali da kuma suka fafata da juna .Sheikh Mahmud Diko ya bayyana muhimmancin da karatun kur'ani da kuma riko da alkur'ani yake da shi da kuma al'adar al'ummar kasar ta Mali na aiki da kur'ani mai tsarki da kuma alfanon da ke tattare da hakan.
928264