Bangaren siyasa da zamantakewa: a yau ne za a fara gudanar da wani taron karawa juna sani da bincike ka waki'ar ranar ashura da zubar da jinin da aka yi a wannan yanki kuma wannan taro nay au sha biyar ga watan Dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya za a gudanar da shi a Makarantar ilimi ta Muhammadiya Tapa Salam a garin Kabul fadar mulkin kasar afganistan.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a yau ne za a fara gudanar da wani taron karawa juna sani da bincike ka waki'ar ranar ashura da zubar da jinin da aka yi a wannan yanki kuma wannan taro nay au sha biyar ga watan Dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya za a gudanar da shi a Makarantar ilimi ta Muhammadiya Tapa Salam a garin Kabul fadar mulkin kasar afganistan.Wannan taron karawa juna sani na addini zai hada malaman addini da masu bincike da nazari da wakilan majalisar dokokin kasar ta afganistan da wakilan cibiyoyin al'adu na wannan kasa da za su tattaunawa da nazari kan wannan lamari na waki'ar ashura.Said Ja'afar Adali Huseini mukaddashin cibiyar al'adu da yada addinin Musulunci da manzon rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa ya zo da shi a cikin jawabin day a gabatar ya bayyana cewa; a cikin wannan taron karawa juna sani da ilimi za a tabo maganar bad a amsa shubhat kan azadari na Imam Huseini (AS) da kuma rawar da Ashura ke takawa wajan kara yan uwantaka a tsakanin musulmi da kuma Hadin kai a tsakanin musulmi kuma da sauran batutuwa da za a tattauna a wajan wannan taron karawa juna sani da ilimi kan abubuwan da suka wakana a ranar ashura a wannan yanki na Karbala.
928857