IQNA

Masu kai Hare-Haren ta'addannaci A Iraki Sun Ce Da Akwai Hannun Amerika

11:34 - January 07, 2012
Lambar Labari: 2252386
Bangaren kasa da kasa:Kungiyar Hizbullah mai gwagwarmaya a kasar Labanon ta fitar da wani bayani da a cikinsa take yin Allah wadai da hare haren bamabamai na ta'addanci da aka kai a ranar sha biyar ga watan Dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a Iraki da jaddada cewa masu kai wadannan hare haren ta'addanci nada hulda ta kud da kud da Amerika.




Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci tai ran ikna ne ya watsa rahoton cewa; Kungiyar Hizbullah mai gwagwarmaya a kasar Labanon ta fitar da wani bayani da a cikinsa take yin Allah wadai da hare haren bamabamai na ta'addanci da aka kai a ranar sha biyar ga watan Dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a Iraki da jaddada cewa masu kai wadannan hare haren ta'addanci nada hulda ta kud da kud da Amerika. Gidan talbijin din Almanar ne ya watsa sanarwar kungiyar ta Hizbullahi da cewa; wadannan sabbin hare haren ta'addanci da bama bamai a kasar ta Iraki wani maida martini ne da Amerikawa ke yi kan kasawar da suka yin a ci gaba da zama a cikin Iraki da fita daga kasar cikin kaskanci da wulakanci da kasa cimma abin da suka raya shi ne ya kai su.Kan wannan dalili ne suka dauki matakin tada bama bamai da yawaita kai hare haren ta'addanci da fakewa da wasu maras kishin kasa da addini da tausayin al'ummar kasar fararen hula.
929828
captcha