IQNA

Bukatar Zartar Da Hukumcin Kisa Kan Dan Kama Karyar Kasar Masar

11:34 - January 07, 2012
Lambar Labari: 2252389
Bangaren kasa da kasa: Mai shigar da kara a kotun da ke hukumta Hussni Mubarak tsohon dan kama karya a kasar Masar a ranar sha biyar ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya bukaci kotun da ta zartar da hukumcin kisa kan hambararran dan kama karyan.




Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci tai ran ikna ne ya watsa rahoton cewa; Mai shigar da kara a kotun da ke hukumta Hussni Mubarak tsohon dan kama karya a kasar Masar a ranar sha biyar ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya bukaci kotun da ta zartar da hukumcin kisa kan hambararran dan kama karyan.Mustapha Suleiman loyan da ke shigar da karar tsohon dan kama karyan a Masar ya bayyana cewa; Husni Mubarak tsohon dan kama karya da kafa zalunci a tsawon mulkinsa a kasar ta Masar ya zartar da kisan kiyashi kan masu gudanar da zanga-zangar nuna adawa da salon mulkinsa a kokarinsu na neman kawo sauyi a kasar dole a zartar da hukumcin kisa kansa da kuma sauran wadanda suka aikata ayyukan kisa tare das hi wato diyansa biyu Ala da jamal da kuma Habib Aladili ministan cikin gida a lokacinsa da mataimakansa shidda. Mai shigar da karar ya kuma soki lamirin yadda kotun take tafiyar da wannan shari'a da yadda take tafiyar gunguru.
929826

captcha