IQNA

Amerika Na Kokarin Rufe Kashin da Ta Sha A Iraki

16:11 - January 08, 2012
Lambar Labari: 2253364
Bangaren kasa da kasa: kungiyar Hizbullah ta gwagwarmaya a kasar Labanon ta fitar da wani bayani dangane da hare haren ta'addanci da fasa bama bamai a kasar Iraki kuma a ranar sha shidda ga watan Dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a birnin Damaskos fadar mulkin kasar Suriya ta fitar da wannan sanarwa da a ciki take Allah wadai da hare'haren ta'addancin.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: kungiyar Hizbullah ta gwagwarmaya a kasar Labanon ta fitar da wani bayani dangane da hare haren ta'addanci da fasa bama bamai a kasar Iraki kuma a ranar sha shidda ga watan Dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a birnin Damaskos fadar mulkin kasar Suriya ta fitar da wannan sanarwa da a ciki take Allah wadai da hare'haren ta'addancin da cewa: akwai hannun Amerika a cikin kai wadannan hare haren ta'addanci da fasa bama bamai na kisan kiyashi domin ta haka ne suke son boye kasa cin nasara da suka yi a kasar iraki da ficewarsu daga Irakin cikin kaskanci da kumya.Wadannnan hare hare da ake kai wa a cikin kasar ta Iraki jim kadan da ficewar sojojin Amerika daga iraki na nuni da cewa wata babbar kasawace ta amerikja a kasar Iraki da kuma yadda ta kulla makirce da hada baki da kungiyoyin yan ta'adda da wadanda suka saba kai irin wadannan hare hare na rashin tausayi da kisan kiyashi kan fararen hula a ciki da wajan kasar ta Iraki. Kuma abubuwan da ke faruwa a Iraki na nuni da cewa Amerika ba za ta taba cimma bakar manufarta a yankin ba kuma za ta yi kunya a yankin.
930114
captcha