Bangaren siyasa da zamantakewa; wakilin reshen jami'ar Almustapha (SWA) al'alamiya a garin Tananarevo na kasar Madagaskar ya shirya gudanar da taron cike kwanaki arba'in da juyayin shahadar imam Huseini (AS) .
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: wakilin reshen jami'ar Almustapha (SWA) al'alamiya a garin Tananarevo na kasar Madagaskar ya shirya gudanar da taron cike kwanaki arba'in da juyayin shahadar imam Huseini (AS) .A ranar ashirin da hudu ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne za a gudanar da taron tunawa da cika kwanaki arba'in da shahadar Imam Huseini (AS) kuma za a samu halartar dalibai na makarantar Imam Sadik (AS) da na kamarantar ilimi dahura da ke karkashin kulawar wakilin reshen jami'ar Mustapha (SWA) al'alamiya a kasar Madagaskar da kuma madarasatul Islami ta darul Hikma suka shira .A lokacin wannan taron na juyayin cika kwanaki arba'in da shahadar imam Huseini (AS) za a gudanar da jawabai na juyayi da kuma kawo tarihin imam Huseini (AS) da gwagwarmayar da yayi da kuma kokarinsa na kare addinin musulunci da yada ilimi da tafarkin kakansa ma'aikin Allah mai tsira da amincin Allah ya tabbata a gare das hi da kuma alayan gidansa tsarkaka.
930378