IQNA

Jam'iyar Musulunci A Azarbaijan Ba Zata Canja babbar Manufarta Ba

16:10 - January 08, 2012
Lambar Labari: 2253369
Bangaren siyasa da zamantakewa; jagoran jam'iyar musulunci a kasar Azarbaijan na riko ya jaddada cewa; muna kokarin ganin mun cimma nasara a babban burin da muka sanya a gaba kuma a dabi'ance dole mu rika gamuwa da matsalolin a hanyar isa ga wannan burin da muka sanya gaba kuma za mu jurewa duk wata matsala da muka fuskanta.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: jagoran jam'iyar musulunci a kasar Azarbaijan na riko ya jaddada cewa; muna kokarin ganin mun cimma nasara a babban burin da muka sanya a gaba kuma a dabi'ance dole mu rika gamuwa da matsalolin a hanyar isa ga wannan burin da muka sanya gaba kuma za mu jurewa duk wata matsala da muka fuskanta.An nakalto daga Aran Neus cewa Alcin Manaf Uf shugaban jam'iyar na riko ya bayyana cewa: kama da tsare Samdaf shugaban jam'iyar musulunci a kasar Azarbaijan da kuma wasu gomomi daga cikin malaman addini a kasar saboda sun nuna adawarsu ta hana mata masu sanye da hijabi shiga makarantu abin yin Allah wadai kuma kamin da tsare su da aka yi wani anin jinjina masu ne kuma nasara ce a gare shu ko shakka babu .Manaf Uf ya jaddada cewa: yadda muka gan wadanda aka kama da tsare su cikin karfi da jarumta lokacin da suka halarci zaman kotu ya kara mana karfin jiki da na rufi kuma muna alfahari das u kuma daga karshe gaskiya ce za ta ci nasara ko shakka babu.
930462
captcha