Bangaren kasa da kasa: shugabannin gwamnatin a kasar jamus a dalilin karuwar rubuce rubuce da maganganun batanci da nuna adawa kan addinin musulunci da wasu shafuka na wasu kungiyoyi masu tsananin adawa da addinin musuluci a shafinsu ke yi domin sani da binciken karuwar wannan matsala na nunawa musulmi karan tsana a nahiyar turai za ta rika sa ido kan irin wadannan shafuka.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; shugabannin gwamnatin a kasar jamus a dalilin karuwar rubuce rubuce da maganganun batanci da nuna adawa kan addinin musulunci da wasu shafuka na wasu kungiyoyi masu tsananin adawa da addinin musuluci a shafinsu ke yi domin sani da binciken karuwar wannan matsala na nunawa musulmi karan tsana a nahiyar turai za ta rika sa ido kan irin wadannan shafuka.Ola Yalpaka dan majalisar dokoki daga jam'iyar masu sausaucin ra'ayi a majalisar dokokin kasar ta jamus' ne a ranar goma sha tara ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiyasa ya bayyana cewa; wasu sanarwowi da shafukan kungiyoyi a kasar Jamus bas u kiyaye hakkokin daidaiku ko na jama'a da sanya su cikin hadari saboda nuna wariya da banbancin addini da akida da kuma tsananin adawar da suke nunawa kan hakan. .wannan matakin yin bincike das a ido kan shafukan ya biyo bayan yadda aka yi kisan gilla kan wasu musulmi mazauna kasar ta jamus da wasu yan ta'adda da tsananin nuna adawa kan musulmi suka aikata wannan kisan gilla na ta'addanci.
932102