Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na trouvetamosquee cewa, an bude wani sabon shafi na yanar gizo da ke mayar da martani kan ayyukan kyamar muslunci da ake yadawa a cikin shafukan yanar gizo daga kasar Faransa tare da halartar masana wannan bangaren.
Kakakin ma'aikatar shari'a a kasar Iran ya sanar da yanke hukuncin kisa kan dan leken asirin kasar Amurka da aka kame yana gudanar da aikin leken asiri a cikin kasar Iran a yau litinin.
Kakakin ma'aikatar shari'ar ya kara da cewa; kotu ta gamsu da kwararan dalilai da aka gabatar mata a matsayin shaidu kan samun ba'amerike Amir Mirza'i Hekmati dan asalin kasar Iran da laifin gudanar da aikin leken asiri ga kasar Amurka a cikin kasar Iran, don haka kotun ta yanke masa hukuncin kisa, to sai dai Amir Hekmati yana da damar daukaka kara a cikin kwanaki ashirin masu zuwa.
Shi dai Amir Mirza'i Hekmati ma'aikacin leken asiri ne a hukumar leken asirin kasar Amurka ta CIA, kuma bayan shiga hannun mahukunta a kasar Iran ya yi furuci da laifinsa na gudanar da aikin leken asiri a kasar, don haka a yau kotun juyin juya halin Musulunci ta Iran ta yanke masa hukuncin kisa.
932502