Bangaren al'adu da fasaha; da dama daga cikin al'ummomin musulmi a kasashen irin su Koweiti ,Labanon.Katar,Bahrain da kuma kasar Suriya sun karbi fim din tarihi ta Mukhtar kuma sun bukaci a tarjama wannan fim na tarihi a cikin harshen larabci kuma kamar yadda aka nakalto daga bakin matasan larabawa wannan fim din ta tabo bangare mai muhimmanci na tarihin musulunci.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; da dama daga cikin al'ummomin musulmi a kasashen irin su Koweiti ,Labanon.Katar,Bahrain da kuma kasar Suriya sun karbi fim din tarihi ta Mukhtar kuma sun bukaci a tarjama wannan fim na tarihi a cikin harshen larabci kuma kamar yadda aka nakalto daga bakin matasan larabawa wannan fim din ta tabo bangare mai muhimmanci na tarihin musulunci.hatta wasu larabawa mazauna jamhuriyar musulunci ta Iran da ke sha'afa da bin diddigin fina-finan Iraniyawa sun bayyana gamsuwarsu da jin dadinsu da yadda aka shirya wannan fim din da kuma yadda fim din ta shiryu da tsaruwa da kuma ta fito da wasu abubuwa masu muhimmanci da tasiri na tarihin musulunci da kuma za iya kawo sauyi da canji a rayuwarmu ta yau da kullum musamman ta zamantakewa da ta addinin.
933047