IQNA

Libya Da Lebanon Sun Kafa Kwamitin Bincike Kan Makomar Imam Musa Sadr

18:31 - January 14, 2012
Lambar Labari: 2256512
Bangaren kasa da kasa, gwamnatocin kasashen lebanon da Libya sun cimma matasa dangane da makomar Imam Musa Sadr da abokan tafiyarsa biyu ta hanyar kafa wani kwamiti da zai bi kadun wannan batu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, gwamnatocin kasashen lebanon da Libya sun cimma matasa dangane da makomar Imam Musa Sadr da abokan tafiyarsa biyu ta hanyar kafa wani kwamiti da zai bi kadun wannan batu da ya hada dukaknin bangarorin biyu.
Sai kuma wani labarin da ya danganci kasar ta Lebanon da ke cewa, babban Magatarda na Majalisar Doinkin Duniya Ban Ki-moon ya soma wata ziyarar aiki ta tsawon kwanaki uku a kasar Labanan daga yau juma'a, domin tattauna batutuwan da suka shafi rikicin siyasar kasar Syria, da matsayin kotun da kasashen duniya suka kafa domin binciken kisan da aka yi tsohon Firayi ministan kasar ta Labanan Rafikul Hariri da kuma neman gwamnatin Labanan ta karbe illahirin makamai da kungiyar Hizbullah ta mallaka.
A tsawon wadannan kwanaki uku dai, Ban Ki-Moon zai gana da shugaban kasar ta Labanan Mishel Suleman, da Firaministan kasar Najib Mikati, da kuma shugaban Majalisar dokokin kasar Nahbih Beri wanda babban abokin kawance ne ga kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hizbullah, yayin da a gobe asabar zai gana da manyan kwadojin rundunar wanzar da tsaro ta MDD da ke kasar.
To sai dai tun kafin Ban Ki-moon ya isa a kasar, tuni kungiyar Hizbullah ta bayyana ziyarar da cewa al'ummar kasar Labanan musamman ma ma'abota 'yanci ba sa marhabin da ita.
934376


captcha