Bangaren nazari da tunani: an fassara litaffin koyar da akida na ayatullahi Uzma Muhammad takiyi Musbahul Yazdi a cikin yaren rasanci kuma an watsa shi tare da hadin guiwar ofishin yada al'adun jamhuriyar musuluunci tai ran a kasar Rasha.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; an fassara litaffin koyar da akida na ayatullahi Uzma Muhammad takiyi Musbahul Yazdi a cikin yaren rasanci kuma an watsa shi tare da hadin guiwar ofishin yada al'adun jamhuriyar musuluunci tai ran a kasar Rasha. Wannan littafi na akida an yi shekaru ana koyar da shi a fannin ilimi na addini da dalibai day an jami'a ke amfanuwa das hi ,Kuma wannan littafi na akida ko shakka babu zai taimaka matuka gayya da amfanar da al'ummar kasar Rasha masu jin harshen rasanci a ko ina suke a duniya musamman idan aka yi la'akari da abubuwan da ya kumsa na akida da kuma bayanai masu gamsarwa da suka shafi akidar musulunci a daidai wannan lokaci na yada da ci gaban addinin musulunci a tsakanin kasashen turai.
935336