Bangaren siyasa da zamantakewa; Fahid Fadil ya bayyana cewa; makiyan ahlul baiti (AS) zuriyar ma'aikin allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa na fakewa da raya yi wa addinin musulunci hidima da fakewa da daga tutar Kalmar la'ila illahu da cutar da addinin musulunci da musulmi.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Fahid Fadil ya bayyana cewa; makiyan ahlul baiti (AS) zuriyar ma'aikin allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa na fakewa da raya yi wa addinin musulunci hidima da fakewa da daga tutar Kalmar la'ila illahu da cutar da addinin musulunci da musulmi.A ranar ashirin da uku ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci a Suid ya shirya wani taron karawa juna sani a jami'ar Lund da ke kasar day a bawa wannan taron taken Wane ne Huseini? Kuma Mene ne Ashura ? kuma wannan yana nuni da yadda wasu ke jahultar wadannan abubuwa biyu masu matukar muhimmanci musamman a daidai wannan lokaci da zalunci da danniya suka yi wa duniya babakere da mamaye ta matukar aka san wane ne imam Huseini da kuma dalilinsa na tashi da kalubalantar zalunci da kuma abubuwan da suka faru a ashura to abubuwa da dama za a warware su.
935262